✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai harin awa 3 a Birnin Abuja

’Yan bindigar sun shafe kusan awa hudu suna cin karensu babu babbaka dauke da muggan makamai

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu sace mutane ne sun kai hari Rukunin Gidajen Gwarinpa da ke Abuja.

Aminiya ta gano ’yan bindigar sun shiga rukunin gidajen ne da karfe daya na dare har zuwa hudu na Asubahin ranar Litinin, in da suka sace mutanen da ba a gano adadinsu ba.

Duk da bayanai kan lamarin ba su kammala tattaruwa ba, sai dai wani makwabcin wurin da abin ya faru ya ce maharan sun far wa unguwar ne dauke da muggan makamai.

Ya kuma ce bayan makaman zamanin har da su kwari da baka da adduna a hannun ’yan bindigar.

To sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, Josephine Adeh, ta shaida wa Aminiya cewa ’yan fashi ne ba masu garkuwa da mutane ba, kuma tuni suka tura wata tawagar ’yan sanda domin ci gaba da bincike.