✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari ofishin EFCC

Wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari ga ofishin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati…

Wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari ga ofishin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da misalin karfe 5:00 na safiyar shekaranjiya Laraba.

’Yan bindigar dauke da miyagun bindigogi sun bude wa karamar hedkwatar Hukumar EFCC da ke Wuse Shiyya ta 7, kafin jami’an tsaron ofishin su mayar musu da martani.

Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce, maharan sun lalata motocin da aka ajiye a harabar ofishin, kafin su tsere ta wata kofa tare da barin wata ambulan dauke da sakon barazana ga Ishaku Sharu, wani babban mai bincike na hukumar.

Ishaku wanda yake shugabantar sashin yaki da almundahanar kudin musayar kudaden wajem shi ne yake jagorantar binciken da ya shafi wadansu manyan ’yan siyasa da manyan sojojin da suka yi ritaya.

Harin ya zo ne bayan makonni da aka harbi wani mai bincike na hukumar, Austin Okwor wanda aka yi masa rauni a harbon da aka yi masa a Fatakwal ta Jihar Ribas.

A tattaunawar da Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya yi da Aminiya a kwanan nan ya bayyana cewa alumdahana ta juyo tana yakar hukumar.

Hukumar EFCC ta ce an kai rahoton harin ga ’yan sanda domin gudanar da bincike a kai.