✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai hari NDA, sun kashe soja, sun sace hafsoshi

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu manyan sojoji

’Yan bindiga sun kai hari barikin sojojin da ke Kwalejin Horar da Kananan Hafsoshin Soji (NDA) da ke Afaka a Jihar Kaduna inda suka kashe wani sojan ruwa.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu manyan sojoji masu mukamin Manjo guda biyu.

’Yan bindigar, wadanda suka shiga NDA tun wajen misalin karfe 1:00 na dare na cikin harabarta har zuwa lokacin da muka kammala wannan rahoton.

Wata majiya mai tushe daga cikin barikin sojojin ta shaida wa wakilinmu cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen barikin saboda a hana maharan fita da sojojin.

“Muna cikin tashin hankali, ’yan bindigar sun dauki numfashin mutane lokacin da kowa ya ke bacci sannan suka kawo hari.

“Yanzu haka an kulle ilahirin barikin ba shiga ba fita, saboda a hana su fita daga ciki kuma an yi ittifakin suna ciki har yanzu,” inji majiyar.

Daya daga cikin sojojin da aka jikkata a harin, yanzu haka dai yana can ana kula da shi a asibitin da ke cikin barikin.

Majiyar ta ce ana fargabar maharan za su iya kashe sojojin a kokarin da suke yi na guduwa.

Da wakiliyarmu ta tuntubi mai magana da yawun NDA, Manjo Bashir Jajira bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.