✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai hari mahaifar Shugaban Majalisar Zamfara

Sun kashe mutum biyu sun sace dabbobi tare da kone rumbunan abinci

Mahara sun kashe mutum uku a wani harin da suka kai a kauyen Magarya da ke Karamar Zurmi ta Jihar Zamfara.

’Yan bindigar sun kona rumbunan abinci tare da sace shanu sama da guda 100 a kauyen, inda nan ne mahaifar ta Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Nasiru Muazu Magarya.

“Sun kai hari garin suna harbin mazauna, suka kashe mutum biyu, suka sace shanu sama da 100 tare da cinna wa rumbunan abinci wuta,” inji wani dan Majalisar Dokokin Jihar.

Bayan harin ne Shugaban Majalisar, Alhaji  Nasiru Mu’azu Magarya ya jagoranci tawagar Majalisar zuwa garin ganin irin barnar da aka yi da kuma jajantawa game da harin.

Bayan Hakimin Magarya Marafa, Alhaji Muhammadu Sani ya zaga da shi tare da bayyana damuwa game da yawaitar hare-haren, Shugaban Majalisar ya yi alkarin ganin wadanda suka aikata barnar sun fuskancin hukunci.

Ya yi wa iyalan wadanda aka kashe ta’aziyya da kuma jaje ga wadanda aka sace dabbobinsu ko aka kona musu rumbunan abinci.

Shugaban Majalisar ya kuma ba wa al’ummar tabbacin ganin an kawo karin jami’an tsaro a yankin domin samar da aminci da kuma cafko miyagun.