✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai hari Kano, sun sace wata mata bayan kashe mutum daya

Wasu ’yan bindiga sun harbe wani mutum sannan sun sace wata mata mahaifiyar wani dan kasuwa, Alhaji Yusuf Jibrin a garin Rurum da ke Karamar…

Wasu ’yan bindiga sun harbe wani mutum sannan sun sace wata mata mahaifiyar wani dan kasuwa, Alhaji Yusuf Jibrin a garin Rurum da ke Karamar Hukumar Rano a Jihar Kano.

Wani mashaidin wannan lamari ya ce ’yan bindigar sun far wa kauyen ne da misalin karfe daya na daren ranar Alhamis inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Daga bisani maharan suka yi awon gaba da mahaifin dan kasuwar, Alhaji Jibrin da mahaifiyarsa, Hajiya Asabe Jibrin.

Aminiya ta samu cewa maharan sun saki mahaifin dan kasuwar wanda ya samu raunuka yayin harin, amma sun yi awon gaba da mahaifiyar tasa.

Majiyar rahoton ta ce mutumin da aka harba, Abba Yusuf Gwaddu ya mutu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano a ranar Laraba yayin da yake jinya.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa, ya inganta rahoton yayin da wakilin Aminiya ya tuntuba.

Haruna ya ce mutane biyu aka yi garkuwa da su amma jami’ansu sun ceto mutum daya kuma suna ci gaba da fadin tashin ganin an ceto matar da lamarin ya rutsa da ita.