’Yan bindiga da ake kyautata zargin ’yan kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya ne sun kai hari a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Imo da wani gidan yari a Owerri, babban birnin Jihar.
Maharan cikin jerin gwanon motoci goma sun fi karfin jami’an tsaron da ke wurare biyu, suka kuma saki fursunoni a gidan yarin bayan sun cinna wa wasu sassan Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan wuta.
- Abin da ya sa ’yan bindiga suke hakon Kaduna – El-Rufa’i
- Abin da muka tattauna da Obasanjo — Sheikh Gumi
’Yan kungiyar ta IPOB sun kona daukacin motocin da ke Hedkwatar Rundunar sannan suka kai farmaki kan ofishin Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar (CID) da ke kusa, suka saki duk mutanen da ake tsare da su.
Wurin da kawai ba su kutsa ba shi ne Sashen Yaki da Satar Mutane a Ofishin na CID.
Jerin gwanon motocin ’yan bindigan sun kuma kai hari kan sojojin da ke sintiri a Umuorji a kan babbar hanyar Owerri zuwa Onitsha, inda suka kona motar sojojin da suka ja da baya.
Majiyoyi sun ce tun karfe daya na dare maharan suka rika cin karensu babu babbaka a garin na tsawon awa biyu kafin wayewar garin ranar Litinin.