✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari dab da barikin soja da ke Jaji

Kwamanda Kwalejin AFCSC ya tabbatar da harin ga Hedikwatar Tsaro

Wasu ’yan bindiga ne sun addabi mazauna da ke makwabtaka da barikin sojoji da ke Jaji a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin Jaji ya ce maharan sun kai hari a kusa da Kwalejin Shugabancin Soji na AFCSC tare da cin karensu babu babbaka a kauyukan da ke kusa da shi, suka yi awon gaba da dabbobi masu yawa.

Kwamandan AFCSC, Air Marshal Olayinka Alade, ya tabbatar da hakan lokacin da yake bayani a Hedikwatar Tsaro a Abuja a ranar, cewa, “Na samu labari cewa jiya Talata ’yan bindiga sun kai hari sun yi awon gaba da dabbobi a kauyukan da ke daura da kwalejin. A lokacin kuma sojin NASI na gudanar da atisayen, shi ne suka yi artabu da su, suka yi musayar wuta.”

Wasu majiyoyi a Jaji zargin maharan sun kai farmakin ne da nufin yin garkuwa da ma’aikatan AFCSC da wasu al’ummomin da ke makwabtaka da shi.

AFCSC babban kwalejin soji ne da ke horas da hafsoshin sojojin sama, na kasa da na ruwa daga sassan duniya har ma da sauran hukumomin tsaro, kuma barikin na da matukar gaske ta yadda wasu al’ummomin fararen hula ke zaune a kan filayensa.

Air Marshal Olayinka Alade ya ce hukumomin soji da sauran na tsaro sun fara daukar mataki a kan ’yan bindigar da suka saje da al’ummomin da suke zama a cikin kasar Kwalejin saboda tsananin girmansa.

“Wasu al’ummomi suna zaune a kasar Kwalejin, sun kuma zama bangarensa. To sai ’yan bindiga suke amfani da damar suna sajewa da mutane,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Amma, kuma sai muka gano cewa a gaba kadan ’yan bindiga sun  mayar da wurin mafakarsu. Saboda haka mun tattauna da Kwamandar Runduna ta 1, kuma zamu share wuraren.”

Harin na baya-bayan nan na zuwa ne mako biyar bayan wasu ’yan bindiga sun kutsa Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka a Jihar ta Kaduna, suka yi garkuwa da dalibai 39.