Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da tsohuwar Akanta-Janar ta Jihar Kuros Riba, Rose Bassey, da wasu mutum uku a kan Babbar Hanyar Calabar zuwa Ogoja da ke jihar.
’Yan bindigar sun kuma harbi wani fitaccen Fasto a jihar, Edim-Edim Omin, wanda yanzu ke kwance a wani asibiti da ba a bayyana ba, ana jinyar sa.
- Kamaru za mu koma muddin Peter Obi ya fadi zaben 2023 – Babachir
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Takaita Cire Kudade Zai Sahfi Zaben 2023
“Wannan lamari ne mai ban tausayi a gare mu kuma yanzu da nake magana da ku, Kwamishinan ’Yan Sanda yana kan hanyarsa don tantance halin da ake ciki da kansa,” in ji kakakin ’yan sandan Jihar Kurios Riba, Irene Ugbo.
Lamarin dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan rundunar ’yan sandan jihar ta sanar cewa ta tura runduna ta musamman don samar da tsaro a kan babbar hanyar.
Kakakin rundunar, wanda ya a ranar Laraba ya tabbatar cewa a ranar Talata ne aka sace mutum hudun, ya bayyana cewa ana kokarin gano ’yan ta’addan tare da kubutar da wadanda abin ya shafa.
Akalla mutum 20 ne aka yi garkuwa da su a tsakanin Uyanga zuwa Ikomita da ke kan Babbar Hanyar Kalaba zuwa Ogoja a cikin watanni biyu da suka gabata.
Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da wasu likitoci biyu, wadanda suka samu kubuta sa’o’i bayan da Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) reshen Jihar Kuros Riba ta tsunduma yajin aiki kan sace su.