Wasu sojoji sun rasa rayukansu yayin artabu da ’yan bindiga a yankin Masarautar Zuru da ke Jihar Kebbi.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffery Onyeama ya kai ziyara Birnin Kebbi, babban birnin jihar a ranar Laraba.
- Wani ya harbe jaririyarsa saboda ba ya son fara haihuwar mace
- Mutumin da aka yi wa dashen zuciyar alade ya mutu
Harin ya faru ne kwana daya bayan da ’yan bindiga suka kashe ’yan sa kai 63 a yankin na Zuru.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Babale Yauri, ya shaida wa manema labarai cewa dakarun tsaron sun fafata ne da maharan, amma bai fadi yawan jami’an sojin da aka kashe ba.
Ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da tumke damararta don ganin ta shawo kan matsalar tsaro da ta addabi Kudancin jihar.
Ya ce, “a cikin kwanaki uku da suka gabata, mun rasa akalla yan sa kai 65, kuma haka ma a jiya mun rasa wasu dakarun soji da ke aiki tare da su.
“Matsalar hare-haren ’yan bindiga tare da garkuwa da mutane don neman kudin fansa ba sabon abu ba ne a Jihar ta Kebbi, amma idan aka yi la’akari da yadda ake musu ruwan wuta a Jihar Zamfara da ke makwabtaka da mu, lallai suna fuskantar babban kalubale daga bangaren dakarun soji da ya sanya suke kwararowa yankin Kudancin jiharmu ta Kebbi.”
A nasa bangaren, Ministan ya ce ya ziyarci Jihar Kebbin ce bisa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar dangane da kisan yan sa kai da aka yi a jihar.
Onyeama ya ce Shugaba Buhari yana kira ga gwamnati da al’ummar jihar da su tsaya tsayin daka wajen tunkarar kalubalen ’yan bindiga.