✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe sojar ruwa, sun sace danta a Jos

Rundunar ’yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kisan wata tsohuwar sojar ruwa, Helen Godos, a kauyen Don da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.…

Rundunar ’yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kisan wata tsohuwar sojar ruwa, Helen Godos, a kauyen Don da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.

Kakakin rundunar DSP Alfred Alabo, ne ya bayyana hakan ga Aminiya, ya kuma ce jami’an tsaro na nan na bin sawun mutanen.

’Yan bindigar dai sun far wa gidan da margayiyar ne da misalin karfe 8:00 na daren jajiberin Kirsimeti, domin sace danta.

Kuma da shigar su unguwar suka kama harbi kan mai uwa da wabi, sannan suka yi wa gidan tsinke.

Wani da lamarin ya faru kan idonsa ya bayyana wa Aminiya cewa matar ta yi ta rokonsu su kyale mata danta amma suka ki.

“Tana ta rokonsu su taimake ta su sakar mata da, amma suka ki, amma daga karshe ma suka harbe ta har lahira nan take.

“Bayan ita ma akwai wani dan gidan da suka harba a kafa, sannan kuma suka tafi da dan marigayiyar.

“Da fitar su suka hau harbin iska don mutane su ba su hanya, sannan suka gudu a babura da motar da suka zo da ita.”

Wannan lamari dai ya jefa tsoro da firgici a zukatan al’ummar yankin kamar yadda suka bayyana wa wakilinmu.