✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun harbe mutum 5 a Kaduna

’Yan bindigar sun afka garin ne inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

’Yan bindiga sun harbe mutum hudu da kuma raunata daya a wani sabon hari da suka kai garin Kerawa a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna. 

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kashe wani mutum daya a Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar.

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna ce ta tabbatar da hakan cikin wani sako da ta wallafa ranar Lahadi, 2 ga watan Janairun 2022 a shafinta na Facebook.

Sanarwar ta ce ’yan bindigar sun afka garin ne inda suka yi ta harbi kan mai tsautsayi wanda a sanadiyyar haka wasu mutane hudu suka rasa rayukansu.

Ma’aikatar ta bayyana sunayen mutanen da aka kashe a Igabin da suka hada da Lado Shuaibu, Usman Haruna, Ayuba Muntari da kuma Jafar Abdullahi.

Haka kuma, ta ce an jikkatar da wani mutum mai suna Mamuda kari a kan satar abinci da babura da ’yan bindigar suka yi a garin.

A daya bangaren kuma, Ma’aikatar ta ce ’yan bindigar da suka kai hari Unguwar Rimi-Afana da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf, sun harbi wani mai suna Joshua Kawu a kirjinsa, wanda bayan an garzaya da shi asibiti likitoci suka tabbatar ya riga mu gidan gaskiya.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Kwamishinan Ma’aikatar, Samuel Aruwan, ta ce Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya kadu da wannan lamari, inda ya jajanta wa ’yan uwa da al’ummar yankunan biyu da lamarin ya shafa.