✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe mutum 15 a Neja

Mahara sun hallaka mutum 15 a wani hari da suka kai a kauyen Ukuru da ke Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja. ’Yan bindigar sun…

Mahara sun hallaka mutum 15 a wani hari da suka kai a kauyen Ukuru da ke Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.

’Yan bindigar sun da suka shiga kauyen sun yi ta harbi kan mai uwa da  inda suka kashe yawancin mutanen da ke karyawa a teburin wani mai shayi.

Ana zargin harin ramuwar gayya ce saboda a kwanakin baya ’yan bangar garin sun dakile harinsu har suka kashe hudu daga cikin maharan.

Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun bari sai da majiya karfi a garin suka tafi gonakinsu kafin suka kai harin suka kuma kwashi dabbobi.

Kokarin wakilinmu na samn karin bayani daga mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Neje, ASP Wasiu Abiodun, bai yi nasara ba.

Jami’in bai amsa kiran da ya yi masa ta waya ba, da kuma amsa sakon kar-ta-kwana da ya tura masa.

Wakilinmu ya kuma nemi jin ta bakin hukumar agaji ta jihar, amma ya tarar jami’an sun tafi lura da aikin samar wa mutanen da ambaliya ta shafi gidajensu a yankin Suleja matsuguni.

A ranar Alhamis Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya yaba wa jami’an tsaro a kokarinsu na ganin bayan ayyukan ’yan fashin daji a jihar.

Sanarwar da ta ce za a yi sansanin soji a jihar, ta ce mutane sun fara komawa harkoninsu a yankunan da ayyukan ’yan bindiga suka tilasta musu yin hijira.