✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun harbe mai juna biyu sun sace mijinta

Sun harbe mai juna biyun sannan suka yi awon gaba da mijinta.

Wasu ’yan bindiga sun harbe wata mai juna biyu murus sannan suka yi awon gaba da mijinta a Karamar Hukumar Offa ta Jihar Kwara.

Lamarin ya faru a ranar Asabar da misalin karfe 7 na dare, yayin da mijin mai suna Lukman da matarsa, Hauwa ke kan hanyarsu ta komawa gida.

  1. Ganduje zai biya wa dalibai 10,000 kudin jarrabawar NECO
  2. Takarar Shugaban Kasa: Fastocin Gwamnan Bauchi sun mamaye Kano

Bayanai sun ce take mai juna biyun ta bakunci lahira, inda daga bisani aka dauke gawarta zuwa Babban Asibitin Offa kuma likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

Sai dai babu wani cikakken rahoton abin da ya sa ’yan bindigar suka kyale surukin Lukman da dansa, wanda suna cikin mota yayin da ’yan bindigar suka bude musu wuta.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’ansu sun bazama wajen ceto mutumin da aka sace cikin koshin lafiya.

“Mun baza jami’anmu domin ceto wanda ’yan bindigar suka sace a yayin da muke ci gaba da fadada bincike,” a cewar Ajayi.