✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun harbe mahalarta casu 8 a Afirka ta Kudu

Wasu ’yan bindiga sun bude wuta kan gungun mutanen da suke murnar zagayowar ranar haihuwa a wani gari a kasar Afirka ta Kudu. Lamarin dai…

Wasu ’yan bindiga sun bude wuta kan gungun mutanen da suke murnar zagayowar ranar haihuwa a wani gari a kasar Afirka ta Kudu.

Lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas tare da raunata wasu uku, kamar yadda ’yan sanda suka bayyana a ranar Litinin.

Mutumin da ake tayawa murna na cikin wadanda aka kashe a harin da aka kai a garin Gqeberha mai tashar jiragen ruwa da ke Kudancin kasar, wadda a da ake kira Port Elizabeth.

“Maigidan gidan yana bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne, wasu ‘yan bindiga biyu da ba a san ko su wanene ba suka shiga tsakar gidan ranar Lahadi da yamma.

“Suna shiga gidan suka fara harbi kan mai uwa da wabi,” a cewar wata sanarwa da ’yan sanda suka fitar.

’Yan bindigar sun “harbe mahalarta bikin ne da gangan,” in ji ‘yan sandan.

“Mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu uku ake ci gaba da fafatawa wajen ceto rayukansu a asibiti.

“Mai gidan wanda ake yi wa bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa na cikin wadanda suka mutu.”

Har yanzu dai ba a san dalilin kai harin ba.

Nomthetheleli Mene, babban jami’in ’yan sandan lardin na gabashin Cape, ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da cewa “wani raini ne ga rayuwar bil’Adama.”

An fara gudanar da bincike kan harin, kuma ’yan sanda sun ce ana farautar wadanda suka kai harin.

Rikici ya zama ruwan dare a Afirka ta Kudu, wadda ke cikin jerin kasashen da ke samun yawan kashe-kashe a duniya, sakamakon tashin hankalin kungiyoyin daban-daban da kuma yawan ta’ammali da barasa.

A shekarar da ta gabata ne aka kai hare-hare da dama a kasar Afirka ta Kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dozin biyu, a wasu wuraren shan barasa daban-daban a unguwannin matsakaicin karfi, a birnin Johannesburg da kuma a gabashin birnin Pietermaritzburg.

Ministan ’yan sanda Bheki Cele, da Kwamishinan ’yan sanda na kasa Fannie Masemola, da kuma kwararrun masu binciken aikata laifuka, sun ziyarci wurin da harin ya faru a safiyar ranar Litinin.