Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun shiga ofishin ’yan sanda na Onueke da ke Jihar Ebonyi, inda suka harbe ’yan sanda uku, sannan suka raunata wasu biyu.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar, Misis Loveth Oda, ta tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin wanda a cewarta ’yan bindigar sun kai farmaki ofishin ’yan sandan ne a daren ranar Asabar.
- An kashe basarake mako daya bayan garkuwa da shi a Neja
- An kama matashi kan yi wa wata fyade a Ebonyi
- Mutum tara aka kashe a rikicin kabilanci a Jihar Ebonyi
Ta ce daga cikin jami’an ’yan sandan da aka kashe akwai Insifekta guda biyu, da kuma wata ma’aikaciyarsu guda daya.
Bayan kashe ’yan sandan, ’yan bindigar sun yi awon gaba da bindigu biyu kirar AK47 daga ofishin ’yan sandan a cewarta.
Misis Loveth ta kuma bayar da shidar cewa, an kai gawarwaki wanda aka kashe dakin ajiyar gawa, sannan a halin yanzu wadanda suka ji rauni na ci gaba da samun kulawa a asibiti.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Mista Stanley Okoroemegha, ya ce gwamnatin jihar tana Allah wadai da wannan harin.
Mista Stanley ya kuma ce gwamnatin ta ba wa jami’an tsaro sa’a 48 su gabatar mata da rahoton yadda aka yi hakan ta faru.