✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe jami’an tsaro 12 a Kaduna

Hukumar tsaro ta Sibl Difens ce ’yan bindiga sun harbe jami’anta 7 da wasu ’yan bijilanti 5 har lahira a wurin hakar ma’adanai a Jihar…

Hukumar tsaro ta Sibl Difens (NSCDC) ta tabbatar da harbe jami’anta bakwai da wasu ’yan bijilanti biyar har lahira da ’yan bindiga suka yi a wurin hakar ma’adanai na Kuringa da ke Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Kakakin NSCDC, Olusola Odumosu ne ya bayyana hakan ga Aminiya ranar Talata a Abuja, inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Litinin da karfe 10:00 na safe.

Haka kuma ya ce jami’in hukumar guda daya ya tsira da munanan raunuka, kuma yana kwance a asibiti yana karbar magani gawarwakinsu kuma an ajiye su a mutuwaren Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna.

Ya ce bayanai na nuna cewa sai da maharan suka kwashe makaman jami’an tsaron kafin su hallaka su.