Hankula sun tashi a Jihar Imo yayin da aka yi wa wasu ’yan kasuwa bakwai kisan gilla da suka fito da yankin Arewacin Najeriya.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, an kashe ’yan kasuwar ne a wasu hare-hare kashi-kashi da suka auku a garin Orlu da kuma Umuaka da ke Karamar Hukumar Njaba a tsakanin ranar Juma’a zuwa Asabar.
Yayin zayyana wa Aminiya yadda lamarin ya kasance, wani shaidar gani da ido mai suna Harisu Umaru Ishiaku, ya ce maharan da suka kai harin yankin kasuwar Afor Umuaka da misalin karfe 8.30 na yammaci, sun yi basaja ne da tufafi irin na sojoji.
Ya ce hudu daga cikin wadanda aka kashe ’yan tsakanin shekara 30 zuwa 45, sun mayar da yankin mazaunarsu na tsawon shekaru aru aru.
Harisu wanda yake zargin baki ne suka kawo wannan hari, ya ce ba a taba samun tsamin dangartaka ba tsakanin wadanda aka kashe da kuma al’ummar yankin na Umuaka ba.
A cewar wani jagoran ’yan kasuwa ’yan kabilar Hausa a Jihar Imo, Malam Ibrahim Abdulkadir, ya ce lamarin na farko ya auku ne a ranar Juma’a a yayin da wasu masu sayar da tsire ke shirin tashi bayan sun kammala cin kasuwarsu ta wannan rana.
Ya ce kwatsam wasu ’yan bindiga a cikin wata mota kirar Sienna suka fara yi musu ruwan wuta na harsashin bindiga.
Haka kuma ya ce, makamancin wannan hari ya sake aukuwa a yayin da wasu ’yan bindiga suka bude wa wasu Hausawa ’yan kasuwa uku wuta a yankin Umuaka na Karamar Hukumar ta Njaba.
A cewarsa, a halin da ake ciki Hausawa ’yan kasuwa da ke zama a Orlu suna rayuwa a cikin fargaba, inda da dama daga cikinsu sun sauya sheka zuwa Owerri, babban birnin Jihar.
Honarabul Ibrahim Sulaiman, hadimi na musamman ga gwamnan Jihar kan al’amuran da suka shafi marasa galihu, ya ce tuni gwamnati da hukumomin tsaro suka shiga lamarin.
Bayan kiran al’umma a kan zaman lafiya, Sulaiman ya ce Gwamna Hope Uzodinma ya nuna kaduwarsa a kan lamarin.
Sai dai neman jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Orlando Ikeokwu ya ci tura, a yayin da bai amsa kiran wayar salularsa ba domin ya tabbatar mana da ingancin rahoton.