✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harba gurneti kan mutane a Zamfara

’Yan bindiga sun harba gurneti kan mutane a Zamfara

Wasu ’yan bindiga a ranar Talata sun harba gurneti mai yawa a garin Birnin Magaji da ke Jihar Zamfara.

Birnin Magaji dai na da iyaka da Karamar Hukumar Batsari da ke Jihar Katsina.

Karamar Hukumar dai na daya daga cikin Kananan Hukumomin da suke fama da ayyukan ’yan bindiga, wanda galibi yaran Dankarami da Ardo Nashawari, wasu kasurguman ’yan bindiga ne suke cin karensu ba babbaka a yankin.

Wani Shugaban ’yan sa-kai a yankin wanda ya yi magana bisa sharadin a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa sai da maharan suka fara farmakar wasu manoma da ke aiki a gonakinsu a gabashin garin tun da farko.

Ya ce, “Bayan manoman sun gudu ba a cim musu ba, sai jami’anmu da ke cikin shiri da makamai, suka kora ‘yan bindigar, nan take kuma aka fara musayar wuta.

“Da ’yan bindigar suka fahimci ’yan sa-kan sun fi karfinsu, sai suka nemi karin dakaru. Nan da nan sai ga wasu gungun mahara a kan babura sun zo, inda suka fara harba gurneti a inda dakarun namu suke.

“A nan ne daya daga cikin gurnetin da aka harba ya fada bai karasa wajen da suke so ba, inda ya fashe a kusa da wani tafki.

“Babu wanda aka kashe ko aka jikkata a harin, amma tilas ta sa maharan sun gudu. Mu ’yan sa-kai dama mun saba fuskantar irin wadannan hare-haren kuma mukan zama cikin shiri saboda mun san kowanne lokaci za su iya kawo mana hari.

“Kashegari an gano ragowar gurnetin da bai fashe ba, inda aka kai shi Fadar Sarki domin a duba shi, kafin daga bisani a damka shi ga jami’an tsaro,” in ji Shugaban ’yan sa-kan.

Duk yunkurin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP, Muhammad Shehu, ya ci tura saboda wayarsa ba ta shiga.

Kazalika, bai amsa sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya tura masa ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.