✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun hallaka wani mafarauci a Kaduna

Maharan sun bindige mafaraucin har lahira.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari a garin Sabon Garin Kudan da ke Karamar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, inda suka kashe wani mafarauci mai suna Hussaini.

Aminiya ta gano cewa maharan sun kai wa garin farmaki ne da misalin karfe 3 na dare, suka yi ta harbe-harbe babu kakkautawa wanda hakan ya tsorata mazauna kauyen.

Wani makwabcin mamacin da ya bukaci sakaya sunansa, ya ce mafaraucin ya fito dauke da bindigarsa ta farauta bayan da ya ji hayaniya ta barke.

“Lokacin da suka fito daga gidansa ya dauka sun yi awon gaba da matarsa, saboda bai ganta ba, sai ya fito da nufin bin bayansu da bindigarsa ta farauta, nan take suka harbe shi,” inji shi.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kuma shiga wani gida a garin inda suka dauke wata matar aure amma daga bisani suka sake ta sannan suka sulale zuwa cikin daji.

A cewar rahotannin, maharan sun bude wa marigayi Hussani wuta ne lokacin da ya fito daga gidansa yana kokarin kai musu farmaki.

Mazauna garin sun shaida wa wakilinmu cewa jami’an tsaro ba su kai musu dauki ba sai bayan da maharan suka tsere.

Tuni aka dai binne mafaraucin kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Zuwa yanzu babu wata sanarwa daga Kakain ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, game da lamarin, kuma bai amsa wayar wakilinmu ba bare mu ji ta bakinsa.