’Yan Bindiga sun kai hari tare da hallaka Sojoji huɗu da ke sintiri a Ƙaramar Hukumar Gudu ta Jihar Sakkwato.
Maharan sun kai harin ne a ƙarshen mako, inda suka jikkata wasu sojoji biyu.
Ɗan Majalisar jihar mai wakiltar Gudu, Yahya Gudu ne, ya tabbatar da kai harin.
Ya ce maharan sun kuma ƙone motocin sintiri biyu na sojojin.
Ya ce, “Eh, gaskiya ne. Wasu ‘yan bindiga sun yi wa sojojin da ke sintiri kwanton ɓauna a kan titin Kukurau zuwa Bangi a ranar Asabar.
“Sun kashe sojoji huɗu sannan suka jikkata wasu biyu. Sun kuma ƙone motocin sintiri guda biyu.”
Gudu, ya bayyana harin a matsayin abin baƙin ciki.
Ya shaida wa Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu game da harin, kuma tuni aka aike ƙarin sojoji zuwa yankin.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun ga ’yan bindiga sun wuce ta yankinsu a kan babura 20.
A cewarsa kowanne babur yana ɗauke da ’yan bindiga biyu kuma ɗauke da makamai.
Ya ƙara da cewar su cutar da kowa ko kuma sace wani a yankin ba, sai dai ba daɗewa suka fara jin ƙarar harbe-harbe.
Daga baya aka gano cewa ’yan bindigar sun yi wa sojojin kwanton ɓauna tare da kashe huɗu daga cikinsu.
Da aka tuntuɓi shi, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Rufa’i Ahmed, ya ce a nemi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojoji ta 8, Laftanar Kanal Ikechukwu Eze, don neman ƙarin bayani.