Wasu ’yan bindiga sun harbe mutum biyar, ciki har da jami’an ’yan sanda uku a gidan Shugaban Karamar Hukumar Katsina-Ala ta Jihar Binuwai, Alfred Avalumum Atera.
Aminiya ta gano cewa maharar sun kuma jikkata karin wasu mutanen da dama a harin da aka kai da misalin karfe 11:30 na safe.
Shaidun gani da ido sun ce harin ya jefa tsoro a zukatan mazauna kauyen da a baya ya shekara kusan biyar yana fama da harin ’yan bindiga, kafin daga bisani sojoji su dawo da zaman lafiya a cikinsa.
Jami’in watsa labarai na karamar hukumar, Tertsea Benga ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa an kai harin ne a daidai lokacin da mutane ke tururuwa zuwa gidan don karbar tagomashin Kirsimeti.
Ya ce harin ya kuma kai ga hallaka mutanen wadanda daya daga cikinsu mai gadi ne a gidan.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar ta Binuwai, DSP Catherine Anene ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.
Ta aiko mana da rubutaccen sako cewa za ta kira waya daga baya amma shiru.