Ana zaman dar-dar a Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja inda mazauna garin Sarkin Pawa suka fara guduwa bayan harin ’yan bindiga da ya kai ga hallaka mutum 30 a yankin.
Aminiya ta gano cewa an kuma sace mata bakwai a garin Sabon Kachiwe yayin harin.
- Gobara ta tashi a gidan talabijin na ARTV da ke Kano
- 2023: Tsarin Karba-karba zai iya samar wa Najeriya baragurbin shugabanni – Sanusi
Wani jami’in Karamar Hukumar, wanda shi ma harin ya shafa amma bai amince a bayyana sunansa ba ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun kuma kone ilahirin kauyen bayan sun karkashe, tare da yi wa duk wanda suka yi arba da shi yankan rago.
Tun da farko dai Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da kai harin a kan kauyukan guda uku.
A cewarsa, an kuma hallaka mutum 13 a Kachiwe, tara a Shape, sai kuma shida a wani kauyen, dukkansu a gundumar Sarkin Pawa da ke Karamar Hukumar ta Munya.
To sai dai wata majiya a yankin ta ce an kone mutum 10 kurmus a dakunansu, yayin da wasu hudu kuma aka yi musu yankan rago a kauyen na Kachiwe kawai.
“Sun kuma yi awon gaba da mata bakwai. Ba zamu iya neman daukin jami’an tsaro ba a lokacin sakamakon katse hanyoyin sadarwar yankin,” inji shi.
Kazalika, majiyar ta ce maharan sun kuma lalata turakun sadarwa mallakin kamfanonin MTN da GLO yayin harin.
Shi ma wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Yanzu haka, ba mu san inda wadanda suka sace matan suka shiga ba, saboda su kansu ’yan bindigar ba su da damar tuntubar mu saboda katse hanyoyin sadarwar. Harin ma ya sami nasara ne saboda ba za mu iya kiran jami’an tsaro ba.
“Bayan sun fita daga kauyukan, sun ci karo da wani mutum da motarsa ta lalace ana yi masa gyara. Da shi da mai gyaran duk sun daure su sannan suka yi musu yankan rago, sai daga bisani aka tsinci gawarwakinsu,” inji majiyar.
Majiyar ta ce an yi wa mamatan sallar jan’iza gaba daya a ranar Alhamis.
Mazauna yankin dai sun roki gwamnati da ta gaggauta dawo da hanyoyin sadarwa a yankin domin su sami damar kiran jami’an tsaro a duk lokacin da aka kawo musu hari.