’Yan bindiga dauke da makamai sun hallaka akalla mutane 18 a gundumar Kuyello ta Karamar Hukumar Birni Gwari a jihar Kaduna.
Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa garin dirar mikiya ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Asabar.
- ’Yan bindiga sun hallaka miji, mata da ’yarsa suna tsaka da ibada
- Dan takarar APGA ya lashe zaben cike gurbi a jihar Neja
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun shafe kusan sa’o’i uku suna ta’asa ba tare da samun kowanne irin dauki daga jami’an tsaro ba.
Da yake tabbatar da lamarin, Kansila mai wakiltar mazabar ta Kuyello, Abdulrahman Yusuf ya ce karin wasu mutum 15 kuma sun sami munanan raunuka.
“Mutum 18 ne aka kashe, 15 kuma sun sami munanan raunuka. Wadanda suke cikin mawuyacin hali za a kai su Kaduna domin ci gaba da samun kulawa.
“Maganar da nake da kai a yanzu haka, muna nan muna shirye-shiryen jana’izar wadanda aka kashe kowanne lokaci daga yanzu,” inji shi.
Ya ce kauyen Kutemeshi na da nisan kimanin kilomita hudu daga garin Sabuwa na jihar Katsina.
Kansilan ya kara da cewa ’yan kato-da-gorar yankin ne kawai suka kaiwa mazauna kauyukan dauki yayin harin.
Abdulrahman ya ce yanzu haka mutanen yankin sun shiga halin damuwa saboda basu san inda za su sa kansu ba.
Sai dai duk kiran da muka yi wa kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna, Mohammed Jalige ba a daga ba.
Kazalika, Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan shima bai amsa rubutaccen sakon da aka aike masa ba kan lamarin ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Ayyukan ’yan bindiga dai ya daidaita mutane da dama a yankin Birnin Gwari da ma wasu sassa na jihar Kaduna.