A Jihar Kebbi, wani hari da ’yan bindiga suka kai Karamar Hukumar Shanga ya yi sanadin kisan mutum biyar tare da barin karin wasu biyar din munanan raunuka.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar dai sun yi wa kauyen Uchukku na Karamar Hukumar kawanya ne da sanyin safiyar ranar Juma’a inda kuma suka harbe mutum biyar har lahira yayin kokarin tafiya da shanu.
Wani mazaunin garin na Shanga, Yusha’u Garba Shanga ya shaida wa Aminiya cewa an kai harin ne da misalin karfe 1:50 na daren ranar ta Juma’a, inda nan take mutum hudu daga cikin wadanda aka harba suka mutu, dayan kuma ya karasa a asibiti.
Malam Yusha’u ya kuma ce yanzu haka mutanen da aka harba suna can a wani asibiti a Karamar Hukumar suna samun kulawa.
A cewarsa, daga cikin wadanda lamarin ya shafa har da wata jaririya wacce ’yan bindigar suka harba a kafa.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Nafi’u Abubakar don jin ta bakin rundunarsu kan lamarin bai amsa kira ko sakon kar-ta-kwanan da aka tura masa ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A wani labarin makamancin wannan, wasu ’yan bindigar sun kai hari kauyen Saminaka da ke Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato inda suka kashe mutum shida.
Aminiya ta gano cewa an kai harin ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, a daidai lokacin da mazan garin, wadanda akasarinsa mafarauta ne, suka fita farauta.
Sai dai babu tabbacin ko harin na da alaka da kisan ’yan bindiga 13 da mutanen garin Tangaza suka yi ranar Asabar bayan an kai musu hari.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa daga cikin mutanen da aka kashe har da wasu matan aure su biyu, yayin da aka yi wa wasu maza su hudu yankan rago.
A ranar Asabar ce rahotanni suka Ambato yadda wasu fusatattun mutanen gari suka babbake wasu ’yan bindigar da suka kashe mutum hudu a garin na Tangaza tun da farko.