✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun hallaka mai juna biyu a hanyar Kaduna

Yan bindiga sun hallaka wata ma'aikaciyar lafiya mai juna biyu na kimanin  watanni takwas a kan babbar hanyar Birnin Gwari

’Yan bindiga sun hallaka wata ma’aikaciyar lafiya mai juna biyu na kimanin  watanni takwas a kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce matar ta rasu ne bayan maharan sun budewa motar hayar da take ciki wuta a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna.

Sun kai harin ne a daidai wani gari mai suna Zankoro dake dab da Unguwar Yako a Karamar Hukumar ta Birnin Gwari, bayan sun budewa motar wuta a kokarinsu na tsayar da ita.

Wani dan uwan marigayiyar, Aliyu Mahmud, shine ya tabbatar da rasuwar matar mai suna A’isha Yusuf.

Ya bayyana ta a matsayin ma’aikaciyar lafiya mai aikin sa kai a yankin na Birnin Gwari.

“Tana da juna biyu na kimanin watanni takwas amma duk da haka jajirtacciya ce.

“Yawancin mutanen yankin suna kaunarta saboda jajircewar ta, duk da cewa aikin sa kai take yi,” inji shi.

Da Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce sai ya kira Baturen ’Yan Sanda na yankin da lamarin ya faru kafin ya ce uffan a kai.

%d bloggers like this: