Wasu daga cikin ’yan uwan wadanda aka sace a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, sun tabbatar da maharan sun fara tuntubar su.
Sai dai sun ce ba su fara neman kudin fansa a wajensu ba, amma sun ba su tabbacin ’yan uwansu na hannunsu.
- ’Yan Najeriya miliyan 95 za su fada kangin talauci a 2022 — Bankin Duniya
- Yadda ’yan bindiga ke neman haramta shige da fice a Kaduna
Wani dan uwa ga daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su mai suna Ibrahim ya ce ’yan bindigar sun kira su a waya tare da ba su tabbacin dan uwansu na tare da su.
“Sun kira mu da misalin karfe 1:00 na ranar Talata, inda suka tabbatar mana da cewa ’yan uwanmu na cikin koshin lafiya a hannunsu su. Sai dai ba su bukaci a biya su kudin fansa ba, amma sun ce za su neme mu.”
Ya kara da cewa hankalinsu ya dan kwanta tun da sun samu labarin inda dan uwansu ya shiga, amma suna cikin damuwa kan kudin da ’yan bindigar za su nema a matsayin kudin fansa.
Kazalika, Aminiya ta samu labarin cewa maharan sun tuntubi iyalan Manajan-Daraktan Bankin Noma, Alwan Hassan, inda suka tabbatar musu da cewar su suka sace shi.
Ita ma wata mata da aka yi garkuwa da ’yan uwanta biyu, Malama Hadiza Gogo, ta tabbatar da cewa ’yan bindigar sun tuntube ta game da inda ’yan uwanta suke.
Ta ce, “Duk da sun hana ni magana da su amma sun tabbatar min da cewa suna cikin koshin lafiya.”
Ta ce ba su nemi kudin fansa a wajenta ba, amma sun bukaci ta zauna cikin shiri a lokacin da za su sake nemanta.
Aminiya ta kuma tabbatar da cewa maharan sun tuntubi mahaifin direban jirgin, inda shi ma suka shaida masa cewar dansa na cikin koshin lafiya.