✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

’Yan bindiga sun fara harbin fasinjojin jirgin kasan da ke hannunsu

Mutumin da ya sa baki ako sako 11 daga cikin fasinjojin ne ya tabbatar wa Aminiya.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja sun harbi daya daga cikin fasinjoijn da suka rage a hannunsu.

Daya daga cikin masu shiga tsakani domin a sako fasinjojin, Malam Tukur Mamu, wanda ya sa baki aka sako 11 daga cikin fasinjojin, ya ce mutumin da aka harba din yana cikin mawuyacin hali bayan harbin da suka yi mishi.

“Ina tabbatar muku da cewa an harbi fasinjan kuma majiya mai tushe ce ta sanar da ni hakan. Za ta iya yiwuwa da gangan suka harbe shi a matsayin wani sako.

“Kashe mutanen da ke hannunsu abu ne da muka san za su iya tunda a baya sun yi barazanar aikatawa,” inji shi.

Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta dauki mataki a kan kari, idan ba haka ba ta shirya daukar alhakin duk abin da ya samu mutanen da ke hannun ’yan bindigar.

Ya bayyana cewa gwamnati na tattaunawa da maharan a-kai-a-kai, amma har yanzu ba ta yi wani kwakkwaran motsi ba.

“Na san abin da ke cikin wannan matsala shi ya sana nake nanata cewa ya kamata Shugaba Buhari ya dauki wasu matakai, marasa dadi, matukar za su kai ga kubutar da rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”

“Da abin da muka samu nasarar yi na bude kofar, gwamnati na da karfin ikon kawo karshen wannan lamari a cikin ’yan kwanaki.

“Na ba su tabbaci cewa hakan za ta samu idan muka samu goyon bayansu, idan kuma ba ta yiwu ba, matukar gwamnati ta yi abin da ya kamata to zan dauki alhaki; abu na gaggaawa irin wannan ba ya bukatara rubuce rubucen gwamnati marasa amfani.”

Shugaba Buhari dai ya sha ba wa jami’an tsaro umarni cewa su kabutar da fasinjojin jirgin kasan ba tare da komai ya same su ba.