✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun dauke uwa da jaririnta a Katsina

’Yan bindiga sun dauke matar aure danta mai wata 17 a kauyen Dandagoro

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar aure danta mai wata 17 a kauyen Dandagoro na Karamar Hukumar Batagarawa, Jihar Katsina.

Mazauna sun ce  ’yan bindiga masu yawan gaske ne suka yi wa kauyen dirar mikiya, suka kutsa gidan da karfin tsiya, suka daddaki masu gadi sannan suka yi awon gaba da matar mai suna Hauwa’u.

“Da suka shiga sai suka yi garkuwa da mai gidan da matar da da daya, amma sai suka kyale mijin a hanya saboda ciwon kafa ta hana shi tafiya da da sauri,” inji wata majiya.

Wasu majiyoyoyi sun ce ’yan bindigar sun tuntubi iyalan matar da aka yi garkuwa da ita suna neman kudin fansa Naira miliyan 30.

Wata majiyar kuma ta ce miliyan biyar masu garkuwar suka bukata amma ana kan tattaunawa da su har zuwa lokacin da ake kammala wannan labarin.

Matar da aka yi garkuwa da ita diyar Dokta Ibrahim Sogiji, wani sanannan malami a Jihar Katsina ce,

Mijinta ne Daraktan Gudanarwa da Harkokin Kudade na Karama Hukumar Mani ta Jihar.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya shaida wa wakilinmu cewa yana jiran bayanin abin da ya faru daga Baturen ’Yan Sanda na Batagarawa.

SP Gambo Isah bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba a lokacin da muka kammala wanna rahoto.

Garkuwar na zuwa bayan kwana guda da sace dalibai 80 da aka yi garkuwa da su a makarantar Islamiyya a Jihar.

Ceto daliban na zuwa ne bayan an ceto wasu 344 da aka dauke su a makarantar GSSS Kankara.

Jihar Katsina, mahaifar Shugaba Buhari ce inda matsalar ’yan bindiga masu garkuwa da mutane ta fi tsanani.

%d bloggers like this: