✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kona gonakin manoman da suka ki ba su ‘haraji’

Suna kuma tilasta wa mutane cire yaransu daga makaranta.

’Yan bindiga a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja sun cinna wa amfanin gona wuta bayan wasu manoman yankin sun ki biyan harajin da ’yan bindigar suka kakaba musu.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane ne ya bayyana hakan yayin da yake karin bayani a Minna, babban birnin Jihar.

A cewarsa, an sami hadin gwiwa tsakanin ’yan Boko Haram da ’yan bindiga a kauyukan Kwaki, Kusaso, Kawure, Chikuba, Kurebe, Madaka, Farin-Dutse, Falali da kuma Ibbru, inda suke tilasta wa mutanen yankin bijire wa gwamnati sannan su cire yaransu daga makaranta.

Ya ce, “Akwai yankunan da muka ga ayyukan ’yan ta’addan na kamanceceniya da na ’yan Boko Haram, matukar suna so su zauna ba tare da an taba su ba, tilas sai sun bi abin da ‘yan bindigar ke so. Duk ranar Juma’a su kan zo masallaci su yi huduba kan mutane su cire yaransu daga makarantu.

“A kwanan nan kuma mun ga yadda wasu ’yan bindigar suke tirsasa manoma su biya haraji kafin su je gonakinsu. Da gangan suke yin haka saboda sun san lokacin girbi ne.

“Idan kuma suka ki biya, su kan cinna wa amfanin nasu wuta, wannan aikin jahilci ne da rashin imani,” inji shi.

Sakataren Gwamnatin ya kuma bayyana damuwa kan cewa Karamar Hukumar Borgu, wacce ke da iyaka da Jamhuriyar Benin ta tasamma zama wani sansani ga ’yan Boko Haram da ISWAP a cikin ’yan watannin nan.

Ya koka kan cewa karancin jami’an ’yan sanda na kara ta’azzara matsalar, inda ya ce jami’an ’yan sanda 8,000 kacal a Jihar, duk kuwa da fadin da take da shi.

Ahmed Matane ya ce abubuwa sun sake tabarbarewa ne a Jihar a ’yan makonnin nan saboda ayyukan da ake yi a Jihohin Zamfara da Kaduna a kan ’yan ta’addan.