✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun bukaci Naira miliyan 10 bayan sun sace malamin asibiti

Wasu ’yan bindiga sun sace wani malamin asibiti a Jihar Gombe a safiyar Talatar da ta gabata, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan…

Wasu ’yan bindiga sun sace wani malamin asibiti a Jihar Gombe a safiyar Talatar da ta gabata, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 10 kafin su sako shi.

Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, shi dai ma’aikacin asibitin mai suna Mista Epharaim Ajuji, shi ne Sakataren wani karamin asibiti da ke garin Hina na karamar hukumar Yamaltu Deba, Jihar Gombe. ’Yan bindigar suna dauke da bindigogin gargajiya da adduna, a lokacin da suka sace shi.

diyar Mista Epharaim, Mary Epharaim ta fada wa wakilinmu a tarho cewa mutanen su bakwai ne suka mamaye gidan nasu, suka tambayi inda mahaifinsu yake. Ta ce sai da suka ji mata rauni, kafin daga bisani su tafi da mahaifin nata.

“Sun shigo gidanmu a daidai misalin karfe 2:30 na dare, suka tambayi inda babanmu yake. Lokacin da ya fito sai suka kama shi, suka kwace mana dukkan wayoyinmu. A lokacn da za su fita daga gidan, daya daga cikin ’yan bindigar sai ya jefo mana wayar babanmu, suka ce za su kira ta domin su yi magana da mu,” inji ta.

Mary ta ce maharani sun bukaci a biya su Naira miliyan 10. “A jiya ne mutanen suka kira mu, daidai misalin karfe 7 na safe ta layin wayar mahaifiyarmu, wacce suka sace, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa. Haka kuma sun yi barazanar cewa za su kashe shi idan aka ki biyan kudin gare su.”

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Gombe, Mista Shina Tairu Olukolu ya ce an sanar da ofishin ’yan sanda na Dadin Kowa cewa wajen karfe 3:30 na dare, bayan da su ’yan bindigar suka yi awon gaba da malamin asibitin. Sai dai ya ce jami’an ’yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun bazama binciken al’amarin kuma nan ba da jimawa ba za su kama ’yan bindigar.