✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun binne gawar matar Sarkin Fulanin da suka sace a Kaduna

'Yan bindigar sun ce iyalanta su yi mata addu'a domin sun riga sun birne ta.

’Yan bindiga sun shaida wa ’yan uwan Sarkin Rugan Ardo da ke unguwar Janjala a Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, Abubakar Ardo, cewa sun birne gawar matarsa ​​da suka kashe a maboyarsu.

Sun kuma bukaci iyalan da su yi mata addu’a.

Wani daga iyalan gidan, mai suna Wakili Usman wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Talata, ya ce shugaban ’yan bindigar, ya bayyana haka ne ga wani dan uwansa, inda ya yi kira ga ’yan bindigar da su ba su gawar matar don birne ta.

Ya ce iyalanta sun roki ’yan bindigar da su saki gawar matar, amma sun yi matukar kaduwa lokacin da shugabansu ya amsa a ranar Litinin cewa, tuni aka birne gawar matar a maboyarsu.

Madakin Janjala, Sama’ila Babangida, shi ma ya tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, “Ina nan a Jere, sai na samu kira daga ’yan bindigar inda sanar da cewa na fada wa iyalanta cewa sun riga sun birne matar Ardo a sansaninsu. Abu na gaba da muka yi shi ne mu yi mata Sallar jana’iza.”

Ya kara da cewa mafi yawan mazauna garin na Janjala musamman mata da kananan yara sun bar garin saboda yadda ake garkuwa da mutane a yankin.

Aminiya ta rawaito cewa ’yan bindigar sun bayyana cewa sun bindige babbar matar sarkin Fulanin, Hulaira Abubakar Ardo, bayan sun karbi miliyan biyu daga hannun iyalanta sai suka saki ragowar kishiyoyinta uku wadanda aka yi garkuwa da su tare.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna kan wannan lamari.