✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun bi wani tsoho gona sun kashe shi

’Yan bindiga sun harbe wani tsoho mai shekara 52 har lahira a lokacin da yake tsaka da aiki a gonarsa a Jihar Neja.

’Yan bindiga sun harbe wani tsoho mai shekara 52 har lahira a lokacin da yake tsaka da aiki a gonarsa a Jihar Neja.

’Yar uwan marigayin ta ce ’yan bindiga sun bude wa dattijon mai suna Samanja wuta ne a lokacin da yake yin shuka a gonarsa ta noman rani a kauyen Baje-Patiko da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja.

Ta ce, “Saboda yawan hare-haren ’yan bindiga yawancin mutanen kauyukan da ke yankin sun bar gidajensu sun koma  gudun hijira a Sarkin-Pawa, hedikwatar Karamar Hukumar Munya.

“Daga Sarkin-Pawa Samanja ke zuwa gonarsa kullu; a ranar Talata da safe, ya je shuka kubewa ne da safe, ’yan bindiga suka riske shi a cikin gonarsa suka kashe shi,” in ji ta.

Ta bayyana cewa daga baya ’yan banga sun je sun dauko gawar daga gonar.

Ta ce kafin rasuwar marigayin, shi ne kadai da na miji da ya rage wa mahaifinsa da ke raye a halin yanzu.