✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun ba mu lambobin waya suna son mu da aure –’Yan Matan Jangebe

’Yan bindigar sun shaida musu cewa suna son su da aure, sannan suka ba su lambobin waya domin su kira su shaida musu ko sun…

Daliban makarantar ’Yan Mata ta Jangebe a Jihar Zamfara da suka kubuta sun ce ’yan bindigar da suka sace su sun ba su lambobin waya tare da alkawarin zuwa gidajensu domin neman aurensu.

’Yan mata da dama da suka tattauna da Aminiya daga cikinsu sun ce ’yan bindigar sun shaida musu cewa suna son su da aure, sannan suka ba su lambobin wayarsu domin su kira su shaida musu ko sun amince da bukatar tasu ko kuma a’a.

Daya daga cikin ’yan matan ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun kuma shawarce su da su yi watsi da karatunsu domin su samu su yi aure.

“Ana dab da suka za su sake mu, sai wasu daga cikinsu sai suka zo suka fara nuna wasu daga cikinmu cewa suna so su aure mu in mun amince, wai bai kamata mu ci gaba da bata lokacinmu da sunan karatu ba,” inji ta.

Sai dai ta ce ’yan bindigar na matukar tsoron jiragen yakin sojoji kuma su kan yi kokarin guduwa domin neman mafaka a duk lokacin da suka ji karar jiragen.

Ta kara da cewa, “Suna yi wa jiragen sojin lakabi da ‘shaho’; idan suka gan su, su kan umarce mu da mu buya a karkashin bishiyoyi da koguna. Gaskiya jiragen na matukar tsorata su.”