✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Hannun agogo na neman komawa baya a Katsina

A makon nan ne ’yan bindiga suka kashe akalla mutum 10 suka sace wadansu a garin Guga da ke Karamar Hukumar Bakori a Jihar Katsina.…

A makon nan ne ’yan bindiga suka kashe akalla mutum 10 suka sace wadansu a garin Guga da ke Karamar Hukumar Bakori a Jihar Katsina.

Wani mazaunin garin mai suna Malam Mahdi Danbinta Guga ya shaida wa manema labarai ta wayar salula cewa cikin wadanda aka sace har da Dagacin garin mai suna Mai Unguwa Ado Hassan da wata yarinya mai shekara biyar.

Sauran mutanen da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su sun hada da Usman Babanyara da Umar Dan’asabe da sauransu.

Ya kara da cewa, “Sun tafi da matata da ’yata mai kimanin shekara biyar. Sun kona gidana da wasu gidajen da shaguna da motoci tare da sace kayan abinci.” Malam Mahadi ya ce ’yan bindigar sun tafi da kaninsa da ’yarsa da kuma surukinsa.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina SP Gambo Isa, ya ce suna bincike kan lamarin kuma za su sanar da zarar sun kammala.

A makon jiya mahara sun kai hari a garin Daddara da kuma Daddarar Liman, inda suka kashe Magaji ’Yangayya da Alhaji Jafaru tare da Bukadinsa da wadansu mutane tare da tasa keyar wadansu zuwa daji da kuma sace dabbobi da kayan abinci da sauransu sannan suka jikkata wadansu.

A wani labarin, mahara sun kai farmaki a garin Magamar Jibiya da ke Karamar Hukumar Jibiya inda suka yi wa DPO mai suna DSP Abdulkadir. A. Rano da kwamandan soja kwanton bauna suka kashe shi, suka harbi sojan a cinya.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya wallafa hoton ta’aziyyar mamatan a kafafen sadar da zumunta, amma bai yi bayani a hukumance ba zuwa yanzu.

Hukumomin ’yan sanda a Jihar Katsina sun ce wadansu jagororin ’yan bindigar, kamar Abdulkarim da Dan Karami da Dangote da Abu Rabe sun dawo kauyen Tsambaye da ke Karamar Hukumar Jibiya bayan sojoji sun matsa musu a jihohin Sakkwato da Zamfara.