Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce babu wani dan bindigar da ke da ’yann kasancewa a raye, don haka wajibi ne a kawar da su daga doron kasa.
El-Rufai ya bayyana cewa Kundin Tsarin Mulki ya riga ya soke ’yancin kasancewa a raye na ’yan bindigar da sauran masu ta’addanci.
- Malami ya yi wa almajirinsa bulala 6,000 a Ilorin
- Damfarar N450m: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi —Ummi Zee-zee
- Matashi ya fille kan kakarsa ya kai ofishin ’yan sanda
- Ana zargin Tambuwal da haddasa rikici a jam’iyyar PDP
Ya ce daukar matakin hana aikata muggan laifuka shi ne mafi tasiri wajen gurgunta ayyukan miyagu kuma duk shugaban da ya san abin da yake yi ya san muhimmancin tsanantawa wajen ragargazar ’yan ta’adda.
Gwamnan ya bayyana wa taro kan tsaron kasa da Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar ta shira cewa babu shugaban da ya san abin da yake ya sa muhimmancin a ci gaba da ragargazra masu aikata manyan laifuka.
“’Yan bindiga suna yakar Najeriya ne kuma babu hanyar tukarar matsalar ta wuce hukumomin tsaro su je su yaki ’yan bindiga a mafakansu su fatattake su kwato dazuka.
“Yawanci hukumomin tsaro sukan dauki mataki ne bayan an kai hari ko an sace mutane; gaskiya yaki muke yi da waddan ’yan ta’addan da ke barazana ga ’yancin Najeriya.
“Saboda haka dole sai hukumomin tsaro sun hada kai sun je sun yake su a maboyansu, su ’yanta dazukan ta yadda ’yan kasa nagari za su riak gudanar da halastattun hahrkokinsu na noma da kiwo.”
A cewarsa, tilas ne gwamnati ta binciko ta kamo ta kuma hukunta duk mutanen da ke hannu a matsalolin tsaron da ke barazana ga diyautar Najeriya.
Don haka ya bukaci a dauki karin jami’an tsaro a kuma wadata su da kayan aiki na zamani domin su kassara ’yan ta’adda; uwa uba a rarraba bangaren shari’a ta yadda za su iya yin hukunci cikin sauki.
Yadda za a kawo karshen
Ya ce, “Hanyar magance matsalar ’yan bindiga masu addabar yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsikiya ita ce aiwtar da Shirin Zamanantar da Kiwo na Kasa (NLTP) da aka samar shekara hudu da suka gabata domin a hanzarta zuba jari a bangaren kiwo tare da hadewa da kuma tsugunar da makiyaya a wasu wurare”.
NLTP ya samar da tsari da matakan da za a bi a zamantar da kiwo a Najeriya da kuma magance rikicin manoma da makiyaya ta hanyar samarwa da kuma karfafa kiwo na nufin tabbatar da dorewa da samun riba mai tsoka a bangaren.
Shirin ya kuma ba da fifiko ga wasu bangarorin tallafi da nufin zamantar da harkar kiwo ta yadda za ta taka muhimmiyar rawar bunkasa tattalin arziki da karin hanyoyin samun kudaden shigar gwamnati.
Sbubwan da shirin ya fi mayar da hankali a kai su ne: magance rikicin manoma da makiyaya; inganta hanyoyin samar da adalci da zaman lafiya; biyan bukatun al’ummomin da abin ya shafa; samar abin yi ga mutane da kuma kula da abubuwan da suka shafi matasa, bincike da kuma samar da bayanai.