’Yan banga sun kashe mai unguwar yankin Adogon Malam a Jihar Neja, Alhaji Sa’idu Abubakar, da kaninsa, Alhaji Salihu Abubakar.
’Yan banga sun yi aika-aikan ne sa’o’i kadan bayan ’yan bindiga sun kai hari kan masu Sallar Asuba a wani masallaci a garin Maza-kuka inda suka kashe mutum 18, suka kuma sace wasu 13.
- ’Ya bindiga sun sanya wa Sakkwatawa wa’adin biyan haraji
- Dogo Gide ya hallaka Damina, kasurgumin dan bindigar da ya addabi Zamfara
Bayan nan ne ’yan banga suka kai farmaki a garin Adogon Malam da safe, inda suka kashe mutanen su biyu.
Garuruwan Adogon Malam da Maza-kuka dai makwabtakan juna ne a Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar hare-haren na ranar Litinin, sai dai ya ce babu tabbaci ko harin na daukar fansa ba ne.
A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta ba da umarnin fadada luguden wuta da sojoji ke kai wa ’yan bindiga zuwa jihar domin dakile hare-haren da ake kai wa al’umma a jihar.
Ya yi wannan kira ne jim kadan bayan harin da aka kai wa masu ibada a masallaci a Maza-kuka ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Yada Labaransa, Mary Noel-Berje, ta fitar, gwamnan ya ce za a iya gamar da ’yan bindiga, a cikin kankanin lokaci, idan aka kai musu hari a lokaci guda.
Ya kuma bayyana cewa ya fara ganawa da shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin duba dabarunsu kan yadda za a dakatar ayyukan ’yan bindiga.