’Yan banga sun kama wasu mutum shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi al’ummar Jihar Nassarawa.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa ’yan bangar sun kai farmaki maboyar ’yan bindigar da ke Tudun Waya a Karamar Hukumar Nasarawa, inda suka ceto wasu mutum bakwai da aka yi garkuwa da su.
- Rashin lafiyar Buhari ta kawo wa gwamnatinsa cikas —Adesina
- Wa’azi: Gwamnatin Bauchi ta gargadi malamai kan tada zaune-tsaye
Wadanda ake zargin sun jima suna garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a hanyar Akwanga, Nasarawa, Eggon da kuma Lafia da ke jihar.
Bayan kama su an kai su hedikwatar ’yan sandan jihar da ke Lafia don ci gaba da bincike gabanin gurfanar da su gaban kuliya.
Nasarar da ’yan bangar suka samu ta sanya mutanen yankin yin dafifi zuwa kallon yadda ake kokarin tafiya da wadanda ake zargin zuwa Lafia.
Da yake jawabi kadan bayan kama wadanda ake zargin, wani mazauna yankin, Mista Bawa Ibrahim, ya jinjina wa ’yan bangar bisa kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro a yankin.
“Mun ji dadin nasarar da aka samu a yau saboda mun jima ba mu yi barci da ido biyu, amma na yi imanin cewa da kama wadannan ’yan bindiga shida da aka yi za mu fara samun zaman lafiya a yankin,” in ji shi.
Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce, “Ba zan iya tabbatar da kama su ba saboda ba a aike mana cikakken bayani kan lamarin ba.”