’Yan banga biyu sun rasu wasu hudu kuma suka samu raunin harbi a musayar wuta da ’yan bindiga a Abuja.
’Yan bangar sun gamu da ajalinsu ne bayan ’yan bindigar sun yi musu kwanton bauna a unguwar Gasakpa da ke Karamar Hukumar Abaji.
- Gobara ta sa an rufe sashen Majalisar Tarayya
- An ba dan sanda kyautar kujerar Hajji saboda mayar da kudin tsintuwa
Wani daga cikin ’yan bangar da ya tsallake rijiya da baya, Ishaku, ya ce lamarin ya faru ne a wani daji da ke tsakanin Abuja da Jihar Neja a ranar Alhamis da La’asar.
Ya bayyana cewa ’yan bangar sun tafi ne domin ceto wani manoma da ’yan bindiga suka dauke daga gonarsa, inda bangarorin suka yi musayar wuta.
Ishaku ya ce ’yan bangar na dab da isa maboyar ’yan bindigar ne bata-garin suka yi musu kwanton bauna, a nan ne suka yi musayar wuta.
Ya ce an dauko gawar mutum biyun da suka rasu, hudun da suka jikkata kuma an kai su asibiti a Lambar, Jihar Neja.
Har muka gama hada wannan rahoto ba mu samu amsar karin bayani da muka tura sako ga Kakakin ’yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ba kan lamarin.
A watannin nan, ’yan bindiga sun tsananta kai hare-hare a yankunan Adagba da Gurdi da Paiko Bassan da Rafin-Daji da ke yankin Abaji.
Yankin na Abaji na iyalan da Jihar Neja ta bangaren Rafin Gurara.