Jama’ar Arewacin Najeriya suna gudanar da gagarumar zanga-zanga kan rashin tsaro da kisan gillar da ’yan bindiga ke yi babu kakkautawa a yankin.
Zanga-zangar ta zo ne bayan Shugaba Buhari ya halarci taron kaddamar da littafin tarihin wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Legas, Cif Bisi Akande, a daidai lokacin da ’yan bindiga suka tare matafiya masu yawa suka kona su kurmus a Jihar Sakkwato, amma bai je ba.
- Kisan Sakkwato: Jama’a sun aike wa Buhari wasikar bacin rai
- Shugaban ’yan banga a Kaduna ‘dan bindiga ne’ —Sojoji
A safiyar Juma’a ce aka fara zanga-zangar a Abuja da sauran wurare, a yayin da ’yan Najeriya ke ta sukar Shugaba Buhari kan nuna halin ko-in-kula da kisan gillar da ake yi a yankin Arewa.
An yi ta caccakar shi kan halartar taron kaddamar da littafin tarihin Bisi Akande a Legas a ranar Alhamis, alhali yana sane da kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa matafiyan a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.
Da dama daga cikin masu sukar shi, sun nemi ya sauka daga mukaminsa, saboda a cewarsu, bai kare rantsuwar da ya yi na kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya ba, sannan ya nuna bai san nauyin da ya rataya a wuyansa ba.
A ranar Alhamis, shugabannin yankin Sabon Birni suka aike masa da wasikar bacin ransu kan yadda gwamnatinsa ta bar ’yan bindiga suka mayar da rayukan jama’arsu ba a bakin komai ba.
Masu zanga-zangar a Abuja za su yi tattaki ne daga Unity Fountain zuwa Majalisar Dokoki ta Kasa, domin bayyana fushinsu kan rashin katabus din gwamnati wajen magance matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya.
Tun a ranar Alhamis, kungiyar Jama’atu Nasril Islam, babbar kungiyar Musulunci a Najeriya ta aike wa Buhari wasikar kar-ta-kwana kan matsalar tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya dai ya shafe shekaru da dama a karkashin gwamnatin Buhari yana fama da matsalar.
’Yan bindiga a yankin sun kashe dubban mutane ciki har da dalibai da mata da kananan yara da jami’an tsaro; Sun yi wa mata fyade.
Sun kuma raba mutane da muhallansu, bayan ga kona gidaje da kadarori da amfanin gona, tare da karbar kudade fansa da ba a iya kiyastawa.