Kungiya kare yankin Arewacin Najeriya (CNG) ta yi Allah-wadai da harin da kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB ta kai wa al’ummar Hausawa a Karamar Hukumar Oyigbo ta Jihar Ribas da ya yi sanadiyyar kashe mutum biyu.
CNG a sanarwar da kakakinta, Abdul’Aziz Suleiman ya fitar ranar Talata a Kaduna, ta yi gargadin cewa dole ne kowace al’umma ta girmama baki da ke zaune a yankinta a matsayinsu na ’yan kasa.
- Sarakunan arewa na taro kan matsalar tsaro
- Abinda ya kamata gwamnati ta yi kan matsalar tsaro a arewa
Ta kuma ce, “Yayin da muke jiran rahoto daga shugabannin ’yan Arewa a Jihar Ribas, muna kara tabbatar wa ’yan Arewa mazauna kowanne sashe na Najeriya cewa ba za mu lamunci cin kashin da ake musu ba.
“Ita kuwa kungiyar IPOB, irin yadda take cin karenta ba babbaka ta hanyar shirya taruka a bainar jama’a ba tare da shayin kowa ba da shirya zanga-zanga, yin barazana tare da aiwatar da abin da ta fada a cikinta, alamace ta irin raunin tsaro da kuma tabbatar da doka da oda a kasa.
“Abin takaici ne yadda Gwamnatin Tarayya da hukumomi a Kudancin Najeriya suka kawar da kai suka kyale kungiyoyi irin IPOB na ci gaba da cin karensu ba babbaka.
“Hakan tarnaki ne ga kokarin gina kasar da kowane dan Najeriya zai zauna a inda yake da bukata.
“Karancin abin da muke bukata shi ne kowane gwamnan Kudu ya fito ya magantu kan hakkin ’yan Arewa na zama ba tare da an kyamace su ba, a tabbatar da ’yancinsu na yin addini, sana’a, adalci da kuma kare su”, inji kungiyar.
Daga nan suka tunatar da jama’a cewa dokar kasa ta tanadai ’yancin zama tare da yin walwala a kowane yanki ba tare da tsangwama ko nuna kyama ba.