✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan APC sun mutu, wasu sun nutse bayan yakin neman zabe a Delta

Mutane biyu sun mutu, uku kuma sun bace bayan yakin neman zaben Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma dan takarar Gwamnan Jihar Delta a Jam’iyyar APC,…

Mutane biyu sun mutu, uku kuma sun bace bayan yakin neman zaben Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma dan takarar Gwamnan Jihar Delta a Jam’iyyar APC, Sanata Ovie Omo-Agege.

Lamarin ya faru ne ranar Talata a unguwar Okerekoko da ke Karamar Hukumar Warri ta jihar, lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida a kwalekwale daga yakin neman zaben jam’iyyar.

“Akwai wasu mutane bakwai kuma da suka jikkata da yanzu haka suke asibiti.

“A iya saninmu magoya bayan APC ne da suka dawo daga yakin neman zaben dan takarar Gwamnan jam`iyyarsu”, in ji wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa.

Ya bayyanawa Aminiya cewa mutane biyu ne suka rasu a hatsarin , sai kuma wasu uku da har yanzu ba a gano su ba.

Daraktan Yada Labaran Kwamitin Yakin Neman Zaben dan takarar gwamnan, Ima Niboro, ya ce Omo-Agege da APC na mika alhininsu ga iyalan wadanda abin ya faru da su, kuma sakamakon hakan sun dakatar da yakin neman zabe har sai abin da hali ya yi.