Daraktan yada labarai na zababben Shugaban Kasa, Festus Keyamo, ya yi zargin akwai shirye-shiryen da jam’iyyun adawa suke yi wajen ganin ba a rantsar da Bola Tinubu ba ranar 29 ga watan Mayu ba.
Keyamo, wanda kuma kuma shi ne Minista a Ma’aikatar Kwadago, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar Asabar mai taken “Zanga-zangar da jam’iyyun adawa ke kokarin yi: Shiru-shiru ba tsoro ba ne.”
- APC ta kori wadanda suka sanar da dakatar da Boss Mustapha daga jam’iyyar
- Uwa ta zargi ’yan sanda da sakin wanda ya yi wa ’yarta ’yar wata 20 fyade
Ya ce ’yan adawar, wadanda ya kira da bata-gari, na kira da ko dai a soke sakamakon zaben, ko kuma a dakatar da rantsar da Shugaban Kasa.
Keyamo ya ce yunkurin nasu ya saba da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma Dokar Zabe, kuma za su iya kawo rudani idan ba a taka musu birki ba.
A cewarsa, “Muna sane da yunkurin da wadannan kiraye-kirayen na rashin kishin kasa.
“Mun kuma san duk yunkurin da wasu daga cikinsu suke yi na yi wa shirin mika mulki zagon kasa,” in ji shi.
To sai dai da take mayar da martani, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana kalaman na Keyamo a matsayin soki-burutsu.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya shaida wa Aminiya a ranar Lahadi cewa ’yan Najeriya na da ’yancin fadin albarkacin bakinsu, amma kada su bari jam’iyya mai mulki ya yi wasa da hankulansu.