✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan adawa ke karfafa batun Biyafara – Pally Iriase.

Mataimakin Babban Mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Mista Pally Iriase ya zargi Jam’iyyar PDP da kitsa fafutikar neman ballewa daga kasar nan da kuma tado…

Mataimakin Babban Mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Mista Pally Iriase ya zargi Jam’iyyar PDP da kitsa fafutikar neman ballewa daga kasar nan da kuma tado da batun sake fasalin kasar nan.

Mista Iriase, wanda yake wakiltar Mazabar Tarayya ta Owan da ke Jihar Edo, ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wata jarida ba Aminiya ba, inda ya ce mambobin jam’iyyar ta adawa ne a sahun gaba wajen jawo rikici a kasar nan.

Ya ce, “Ba matsala ce ta samun sabani ba, wanda a kowane lokaci za a iya samunsa a tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa nake tsoro ba, a’a wadanda suka tsoma kansu  a halin zafafa harkokin siyasa ne abin damuwa; za ka rika jin nau’o’in nuna kabilanci da duk sunan da za ka iya kira, wasu suna son ’yantacciyar kasar Biyafara, yanzu kuma wadansu sun ce suna so a sake fasalin kasa. Wajibi ne ’yan Najeriya su farka su fahimci mugun shirin akasarin ’yan siyasa.”

Ya kara da cewa: “Abin da na fahimta da wadannan kiraye-kiraye na sake fasalin kasa da neman ballewa da sauransu, wata ajanda ce da aka sanya ta matsi saboda yau, idan kuka dubi taron wadanda suke karfafa wadannan kiraye-kiraye za ku ga galibinsu ’yan adawa ne da suka fadi a zaben da ya gabata. A ’yan kwanakin nan na karanta a jaridu cewa shugabannin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da na Tsakiyar Najeriya sun hade kai, da na dubi jerin shugabannin sai na gyada kaina kawai, Allah Ka taimake mu domin kafafen watsa labarai na iya mayar da fanko ya zamo wani abin barazana.”

Mista Iriase ya kara da cewa: “Ina kira ga dukan wadanda suke irin wadannan maganganu cewa suna da wakilai a Majalisar Dokoki ta kasa da majalisun dokoki na jihohi, me ya sa ba za su jawo hankalinsu ba, kan fasalin kasar da suke so a sake ba ta yadda zai zamo yana da masaniya? Don haka idan ka dubi sunayensu, za ka gane cewa wadanda suka fadi a zaben da ya gabata ne suka fi yawa wajen halartar wadancan tarurruka, don haka ’yan Najeriya su yi taka-tsantsan.”