A jihar Legas, an gurfanar da wasu ’yan acaba biyu a gaban wata kotun Majistare bisa zarginsu da lakada wa wasu jami’an ’yan sanda biyu dukan tsiya sannan suka lalata motocin sintirinsu.
Ana dai zargin Jimoh Lasisi mai shekara 43 da Femi Ajayi mai shekara 35 da aikata laifuka hudu masu nasaba hadin baki, cin zarafi da kuma tayar da zaune tsaye.
To sai dai wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin.
Dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Benedict Aigbokhan, ya shaida wa kotun cewa ana zarginsu da ma wasu ’yan acaban da yanzu suka cika wandonsu da iska da aikata laifin a ranar 22 da kuma 25 ga watan Nuwamban 2021, a rukunin gidaje na Jakande da ke Ejigbo.
Ya ce mutanen sun hada baki wajen ji wa ’yan sandan raunuka lokacin da suke bakin aiki.
A cewar dan mai shigar da karar, ’yan sandan da aka lakada wa dukan sun hada da Insfekta Alulu Tunde da Wasiu Isiaka, wadanda ke aiki da ofishin ’yan sanda na Ejigbo.
Insfekta Benedict ya ce wadanda ake zargin sun kuma lalata motocin sintiri na ’yan sandan guda biyu.
Ya ce laifin ya saba da sassa na 44 da na 170(3) da na 250 da kuma na 411 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Legas na shekarar 2015.
Alkalin kotun, Mai Shari’a E. O. Ogunkanmi, ya bayar da wadanda ake zargin beli a kan N500,000 kowannensu da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
Ya kuma ce tilas ne masu tsaya musun su kasance cikakkun ma’aikata masu shaidar biyan haraji ta Gwamnatin Jihar Legas.
Daga nan sai ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2022 don yanke hukunci. (NAN)