✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yakubu Dogara ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yakubu Dogara ya goyi bayan takarar Atiku Abubakar a zaben 2023 da ke karatowa.

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa ta PDP.

Dogara ya samu tarba a cikin jam’iyyar ne a yayin yakin neman zaben Shugaban Kasa da dan takarar jam’iyyar, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi a Jihar Legas.

Wannan dai na zuwa ne sa’o’i 48 bayan Kungiyar Dattawan Arewa ta mara wa Atiku baya a matsayin wanda za su yi  a zaben 2023.

A ranar biyu ga watan Disamba ce kungiyar da ta kunshi shugabannin addinai na Kirista da Musulmi a Arewacin kasar nan ta ce bayan tantance dukkan ‘yan takarar Shugaban Kasa, Atiku ne wanda za ta mara wa baya.

“A bayyane yake cewa jam’iyyar APC na shirin dagula al’amura; don haka ba za ta iya zama jam’iyyar da a yanzu da kuma nan gaba zamu mara wa baya ba.

“Bayan zaben 2023, APC na iya mutuwa murus a matsayin jam’iyyar siyasa.

“Ragowar jam’iyyu biyun (NNPP da LP) za su iya ci gaba da kasancewa masu fafutuka a fagen siyasa a nan gaba, daga dukkan alamu, PDP ce zabin da fi dacewa a marawa baya.

“Abin da kawai ake bukata shi ne a dore wajen magance wasu matsaloli da kalubalen da kasar nan ke fuskanta,” inji kungiyar.

Sai dai amincewar ba ta yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike dadi ba, wanda shi ma ke takun saka da Atiku tun bayan gudanar da zaben fid-da-gwanin jam’iyyar PDP a ranar 28 ga watan Mayun 2022, wanda ya sha kaye a hannun Atikun.

Wike ya soki Ykubu Dogara kan goyon bayan takarar Atiku Abubakar.

Wike da wasu Gwamnoni biyar na jam’iyyar PDP na ci gaba da yin takun kasa da takarar Atiku da kuma shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu.