Tsohon dan kwallon gaba a Super Eagles Yakubu Aiyebgeni da Kalu Uche ne suke sahun gaba a ’yan kwallon Najeriya da suka fi samun albashi mafi tsoka a kasashen Turai.
Wannan bayani yana kunshe ne a wata kididdiga da wata Mujalla ta yi a jadawalin da ta fitar na ’yan kwallon Najeriya da suka fi cabawa wajen samun kudi a sassan duniya.
Kamar yadda bayanin da Mujallar ta kalato kuma ta daddale, ta ce Yakubu da Kalu ne suka fi samun kudi a kakar wasa ta 2014 zuwa 2015 a Nahiyar Turai.
Mujallar ta ce Yakubu ya samu albashin da ya kai Dala miliyan biyu da rabi kwatwankwacin Naira miliyan 562 da dubu 500. Haka shi ma Kalu Uche an bayyana cewa ya samu akalla Dala miliyan 2 da rabi, watau daidai da na Yakubu Aiyegbeni.
Na ukunsu shi ne John Mikel Obi sai dan kwallon Sounder Seattle Obafemi Martins da mujallar ta ruwaito suna samun Dala miliyan 2 kwatankwacin Naira miliyan 450 a shekara kowannensu.