✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yakin Yemen ya ci kananan yara 27 a kwana 10 – UNICEF

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar a cikin kwana 10 an kashe yara kanana 27 a Yemen. A…

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewar a cikin kwana 10 an kashe yara kanana 27 a Yemen.

A wata sanarwa da aka fitar asusun na UNICEF ya fadi cewa an kashe yaran ne a hare-hare ta sama da Kawancen Kasashen Larabawa da Saudiyya ke wa jagoranci suka kai a wani gidan sayar da man fetur mallakar ’yan tawayen Houthi da ke Yammacin San’a Babban Birnin Yemen din.

UNICEF ya bukaci da a dakatar da kai wa fararen hula hari a kasar ta Yemen, inda ya kara da cewa kuma a kasar babu wata matsera ga yara inda mutuwa ke bin su zuwa makarantu, gidaje da filayen wasanni.

An kwashe tsawon shekaru ana rikicin siyasa a Yaman inda watan Satumban 2014 ’yan tawayen Houthi suka kwace iko da San’a Babban Birnin Kasar tare da wasu yankunan daban kamar yadda TRT ta ruwaito.

A watan Maris din 2015 kuma Saudiyya ta jagoranci kasashen Larabawa wajen kai wa mayakan na Houthi hare-hare ta sama domin ba wa gwamnatin kasar goyon baya.