Babban Sakataren Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba za ta kakaba dokar hana zirga zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Ukraine ba.
NATO ta bayyana hakan ne biyo bayan kiraye kirayen da mahukuntar kasar ke yi na taimakawa wajen taka wa Rasha birki a kan luguden wuta da take yi a kan kasar.
- An nada wa Sarki Sanusi rawanin zama Halifan Tijjaniya a hukumance
- Ragamar mulkin Najeriya ta koma hannun Osinbajo —Buhari
A yayin wani taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kasashen NATO, Stoltenberg ya ce hanya daya tilo da za a bi wajen aiwatar da dokar hana zirga zirgar jiragen sama a Ukraine ita ce ta harbo jiragen saman Rasha, kuma yin haka zai kai ga babban yaki a Turai, wanda zai shafi kasashe da dama.
Stoltenberg ya yi kashedin cewa al’amura na iya rincabewa fiye da yadda ake gani a yanzu a kwanaki masu zuwa, inda za a samu karin asarar rai da wahalhalu da barnace barnace, duba da yadda Rasha ke shigowa da manyan makamai tare da ci gaba da hare hare a fadin kasar.
NATO, wadda ta ce wannan yaki ba nata bane, ta dau wannan mataki ne duk da magiyar da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi ta a taimaka masa wajen dakatar da luguden wutar da Rasha ke yi a biranen kasarsa.
Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito Ministan Harkokin Wajen Ukraine Dmytro Kuleba yana gabatar da jawabi ga taron ta kafar bidiyo, inda ya mika bukatar daukar mataki kafin a makara, yana mai cewa a shirye suke su kare kansu, amma suna neman taimako.