✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki na Ruhaniya

“Daga bisani, ku karfafa cikin Ubangiji, cikin karfin ikonSa kuma. Ku yafa dukan makamai na Allah, domin ku samiu ikon da za ku yi tsayayya…

“Daga bisani, ku karfafa cikin Ubangiji, cikin karfin ikonSa kuma. Ku yafa dukan makamai na Allah, domin ku samiu ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaidan. Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulki da iko da mahukuntar wannan zamani mai duhu da rundunai masu ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Afisawa:6:10–12). “Ku yi hankali shimfide, ku yi zaman tsaro; magabcinku Shaidan, kamar zaki ne mai ruri yana yawo yana neman wanda za ya cinye. Ku tsaya masa fa, kuna tabbatuwa cikin ban-gaskiyarku, kuna kuwa sani ’yan uwanku da ke cikin duniya suna shan wadannan azabobi da kuke sha. Allah kuwa na alheri duka, wanda ya kiraye ku zuwa cikin madawamiyar daraja tasa cikin Kiristi, bayan da kun sha wuya ’yan kwanaki da kansa za ya kammala ku, shi kafa ku, shi karfafa ku kuma. A gare shi mulki har zuwa zamanun zamanai. Amin.” (1Bitrus:5: 8–11).

Tabbacin yakin da muke ciki:

Da zarar mutum ya karbi Yesu Kiristi ya zama mai cetonsa, ya kuma yarda da nufin Allah game da rayuwarsa, akwai abin da ya sake shiga ciki kuma; wato yaki. Ko ka gane ko ba ka gane ba; ko ka sani ko ba ka sani ba, gaskiyar ita ce, ka rigaya ka zama daya daga cikin wadanda Shaidan zai yi gaba da su. Duk mutumin da bai karbi Yesu Kiristi ba, Shaidan ba ya bata lokacinsa a wurin, domin ya san da zamansu. Amma da wuya ka ce; ka ba da gaskiya ga Yesu Kiristi, wato ka yarda da hadayar da ya yi a bisa gicciye domin dukan duniya, to ka zama magabcinsa ke nan. Wannan magabtaka za ta ci gaba har sai Yesu Kiristi ya dawo domin ya kai mu sama ko kuwa idan kwananmu ya kare a wannan duniya. Shaidan yana cike da haushi cikin zuciyarsa domin korar da aka yi masa daga cikin sama inda Allah da kansa yake, saboda girman kai da ya nuna a tsakanin mala’iku; yana ganin kamar zai iya rinjayar dukan mala’ikun Allah su bi nasa ra’ayi na nuna wa Allah rashin kunya da taurin kai. Ya san cewa Allah Ya rigaya Ya la’ance shi, kuma ba zai taba samun zarafin tuba ba kuma, ya sani babu dama kuma ya rigaya ya yi latti kuma babu wani abin da zai iya yi, hukuncin Allah na nan rataye bisa wuyansa tun wancan lokacin. Shi ya sa ya ci gaba kawai da irin halayen nan na rudin mutane; da kuma karkatar da tunanin mutane domin ya janye hankulansu daga hanyar bauta wa Allah yadda ya kamata. Wannan yaki tsakanin masu bin Yesu Kiristi da Shaidan ba da wasa ba ne ko kadan, shi ya sa maganar Allah na koya mana cewa: “Daga bisani, ku karfafa cikin Ubangiji, cikin karfin ikonsa kuma.” Gaskiyar ita ce idan ba tare da ikon Allah ba, babu dan Adam din da zai iya cin nasara bisa kowane hari da Shaidan zai kawo; dole ne mu samu karfi daga wurin Allah da kansa. Sai mu tuna fa da cewa; “Gama ko da muna tafiya cikin jiki, ba mu yi yaji bisa ga jiki ba.” (2Kor.10:3).
Yakin da muke ciki na ruhaniya ne ba na jiki ba. Maganar na koya mana cewa: “Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulkoki da ikoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Afisawa:6:12).
Za mu dauki lokaci mu yi bincike a kan wadannan manyan kalmomi ko sunaye:- Mulkoki, Ikoki, Mahukuntar Wannan Zamani da Rundunai masu Ruhaniya na Mugunta cikin Sammai: Ina so mu san cewa wannan magabcin wato Shaidan da kansa yana da cikakken tsari cikin nasa masarautar, kuma suna da hadin kai sosai a cikin dukan muguntar da suka yi niyyar aikatawa. Wannan irin tsarin matsayin da yake da shi ne cikin mulkinsa; kada mu dauka da wasa cewa dukan masu bin Yesu Kiristi, muna sansanin yaki ne a kowane lokaci, kamar yadda akan sa sojoji su yi ta sintiri, ko kuwa kamar yadda soja yake a bakin dagar yaki.
Yin sakaci a irin wannan wuri ba karamin hadari ba ne ko kadan. Wannan irin yakin, maganar Allah na kiransa – yakin kirki ko kuwa yakin imani. “Ka yi yakin kirki na imani, ka ribaci rai na har abada, wanda aka kira ka zuwa gare shi, har kuwa ka furta kyakkyawan furuc ia gaban shaidu masu yawa.” (1Tim.6:12). Yakin kirki, yakin kare ban-gaskiyarmu ce cikin Yesu Kiristi. Niyyar Shaidan ita ce ya ga cewa ya ci nasara a kan duk masu bin Yesu Kiristi ta wurin sa mu mu kafa tunanin a kan abin da muke iya gani da idanunmu, yakan yi kokari sosai ya kawar da tunanin yin imani. Shi Shaidan ya sani ta wurin ba da gaskiya ga Allah Ubangiji za mu iya samun kowace albarka ta ruhaniya; shi ya sa zai yi duk abin da zai iya ya ga cewa tunaninmu bai kai wurin ba. Maganar Allah ta sake tunashe mu cewa: “Ku natsu, ku kuma zauna a fadake. Magabcinku Iblis yana zazzagawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lankwame. Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan ban-gaskiyarku, da yake kun san ’yan uwanku a duniya duka an dora musu irin wannan shan wuya. Bayan kun sha wuya kuma ta dan lokaci kadan, Allah Mai alheri duka, Wanda Ya kira ku ga samun madawwamiyar daukakarSa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, Ya kafa ku, ya kuma karfafa ku. Mulki ya tabbata a gare Shi har abadan abadin. Amin, amin.”(1Bitrus:5:8 -11). Iblis ya dade yana yaki da mutum tun daga farkon halittar dan Adam, domin wannan ya gogu sosai cikin sanin asirin irin wannan yaki.
Abu na farko shi ne; Shaidan ya san mutum da dadewa; ya kuma san dabarar da zai yi domin ya yaudari mutum har ya samu ya ci nasara a kansa. Shi Iblis ya rigaya ya lura da yadda mutum ke tafiya da kuma yadda halin mutum yake, haka nan ya san yadda zai kawo wa mutum farmaki har ya iya cin nasara.