Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar cewa, yaki da rashawa a karkashin tsarin mulkin farar hula na dimokuradiyya da ake amfani da shi a Najeriya akwai wahalar gaske.
Shugaban ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da Gidan Talabijin na Arise a safiyar Alhamis.
- Babu mahalukin da zai sa APC a aljihunsa —Buhari
- Matsalar Tsaro a Arewa maso Yamma ta kai ni bango — Buhari
Buhari ya ce yaki da cin hanci da rashawa ya kasance abu mai sauki a gare shi yayin da yake Shugaban Kasa a zamanin mulkin soja.
“A wancan lokaci, na samu saukin yaki da rashawa don akwai mutane da dama da aka tura gidan kaso gabanin a hambarar da gwamnatina.”
Sai dai ya ce duk da wannan kalubale da yake fuskanta tun bayan zamansa zababben shugaba na dimokuradiyya shekaru shida da suka gabata, gwamnatinsa tana ci gaba da samun nasarori wajen zakulo jami’an gwamnati masu babakare a kan dukiyar al’umma.
“Gwamnatina tana ci gaba da samun nasarar wajen zakulo jami’an gwamnati masu aikata rashawa.”
Shugaban ya kuma bayyana damuwa dangane da halin da Kananan Hukumomi a kasar ke ciki, lamarin da ya ce Gwamnoni sun kashe tsarin Kananan Hukumomin baki daya.
“A yanzu Kananan Hukumomi ba su da wani tsari ballantana tasiri, ba sa iya yin komai a kashin kansu, hatta kudin da ake ba su a halin yanzu ba su da ikon sarrafa su da kansu.
“Idan da ana bai wa Karamar Hukuma Naira miliyan 300 domin gudanar da wani aiki, a yanzu abin da take samu ba ya kaiwa Naira Miliyan 100, wannan fa shi ne halin da Kananan Hukumomin ke ciki,” a cewar Buhari.
Shugaba Buhari ya kuma yi tsokaci dangane da ta’addancin mayakan Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar, inda ya ce lamarin na da babbar nasaba ne da talauci da kuma rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Ya ce galibin mayakan Boko Haram ’yan Najeriya ne kamar yadda Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya sanar da shi.